Daya daga cikin Fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna daya kubuta, Hassan Usman, ya ce har yanzu shi mai goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Kafin a sake shi a ranar 25 ga watan Yuli, Usman wanda ya kasance lauya da matarsa, Amina na daga cikin fasinjojin da aka sace yayin harin da aka kai ranar 28 ga Maris, 2022.
Usman, wanda ya kwashe sama da kwanaki 100 a tsare yana daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su da aka gani a wani faifan bidiyo inda ‘yan ta’addan ke azabtar da su.
Da yake magana da ICIR, Usman ya yarda cewa duk da cewa har yanzu shi mai goyon bayan Buhari ne, amma gwamnatinsa ta samu maki “kasa da matsakaici” ta fuskar tsaro.
Ya ce, “Har yanzu ni mai goyon bayan Buhari ne amma ta fuskar tsaro zan iya sanya wannan gwamnati kasa da yadda ya kamata ya kasance.
DUBA WANNAN LABARIN: Oyetola ya shigar da kara don Kalubalantar nasarar Adeleke
Da yake magana game da abin da ya faru, Usman ya ce, “Wannan abu ne mai daci a rai, da zai ci gaba da bata masa rai idan har ya tuna da su.
Tun lokacin da aka kama mu, sai da muka yi tafiya mai nisa kusan kwanaki uku kafin mu isa sansanin da aka tsare mu, kusan watanni hudu kuma kasancewar akwai wani abu mai zafi a raina a zahirin gaskiya.”
“Saboda tun da muka isa wannan sansani, a mafi yawan lokuta muna kwana a kan babur. ruwan sama, ya sauko mana aka, mun kasance a wannan yanayi.
Sauro da kwaruka, da macizai sun daɗe suna saran mu.
“Mun kashe macizai fiye da 10, da sauran kwaruka masu cutarwa, kamar kunama.”
Har yanzu dai akwai sauran mutane a hannun yan Garkuwa, da suka sace su, bayan farmakar jirgin kasan a watannin baya.