Har yanzu gamayyar jami’an tsaron da ke kula da iyakokin kasa domin tabbatar da dokar kulle iyakokin wanda aka kwashe watanni 16 suna yi, suna ci gaba da kulle iyakokin kasar kwanaki bakwai da umurnin da shugaban kasa ya bayar na bude iyakokin kasar guda hudu ciki kuwa harda iyakar Seme.
Gamayyar jami’an tsaron da ya hada ‘yan sanda, sojoji, jami’an lura da shige da fice, kwastan, NSCDC, na ci gaba da amfani da dokar farko ta hana shigo da komai a kasar wacce aka ayyana a cikin watan Agustan 2019.
Wadannan jami’ai kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana na ci gaba da lura da atisaya a Owode da kuma Seme har zuwa ranar Laraba.