Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya da ke yajin aikin ta ce tana jiran martanin gwamnatin tarayya kan bukatun ta.
Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa kwamitin sulhu na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs ya gana da shugabannin kungiyar ASUU a ranar Litinin din da ta gabata.
A ci gaba da tattaunawa da kungiyar ta ASUU kan batun yarjejeniyar kungiyar ta 2009 da kuma wasu bukatun kungiyoyin jami’o’i hudu, wadanda a halin yanzu suke yajin aiki.
Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa taron ya yi daidai, yana mai cewa suna sa ran gwamnati za ta mayar da martani kan batutuwan da suka tattauna da kwamitin.
Da aka tambaye shi ko ASUU za ta janye yajin aikin nan ba da dadewa ba tunda ta yi tattaunawa ta gaskiya da kwamitin Briggs, Osodeke ya ce, ‘’Ban sani ba ko za mu janye yajin aikin nan ba da dadewa ba. Muna jiran amsa ta karshe daga gwamnati.”
ASUU ta fara yajin aikin ne a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, bayan da gwamnatin tarayya ta gaza biyan wasu bukatunta da suka hada da, sakin kudaden farfado da jami’o’i, sake tattaunawa da yarjejeniyar FGN/ASUU a shekarar 2009, sakin alawus-alawus da malaman jami’o’in suka samu, da kuma biyan albashin da suke nema.