Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyar PDP ta gane kura-kuran da aka tafka a baya, kuma tana aiki tukuru domin samun daukakar da ta bata.
Atiku wanda ya je Gombe domin halartar bikin aure, ya bude wani ofishin yakin neman zabe a takaice domin tabbatar da burinsa na zama dan kasa lamba daya a 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ya Nada Gwamna Buni Mashawarci Na Musamman
Wakilinmu ya rawaito cewa Jamilu Ishaku ne wanda ya zo na farko a zaben fidda gwani na gwamna a PDP na 2023 ya bayar da gudummawar ofishin.
Har ila yau, Ishaku ya bayar da gudummawar kimanin motocin yakin neman zaben guda 10.
Da yake bayyana damammakin jam’iyyar PDP a wata hira da ya yi da ‘yan jarida a filin jirgin sama na Sani Abacha Gombe, Abubakar ya bayyana damar jam’iyyar a matsayin babba saboda gazawarta.
Ya yarda cewa jam’iyyar ta yi rashin nasara a shekarar 2015, biyo bayan abin da ya kira kurakurai, wadanda PDP ta farfado daga ciki.
Abubakar ya ce, “PDP jam’iyya ce mai farin jini kuma ita ce jam’iyya mafi tsufa a Najeriya. Mun gane cewa mun yi kuskure.”
Da yake magana kan yiwuwar jam’iyyar a zaben 2023 a cikin rigingimun cikin gida a babbar jam’iyyar adawa, Abubakar ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.
“Har yanzu ina magana da ƴan jam’iyyar da suka fusata kuma na yi imanin a ƙarshen ranar za mu yi aiki tare,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Najeriya @62: Buhari Bai Barwa ‘Yan Najeriya Abin Da Zasu Yi Murna Dashi Ba – LP
Shugabancin jam’iyyar Labour LP ya yi wa gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari kaca-kaca, na barin talakawa ba tare da abinda za su yi murnar cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Abayomi Arabambi ya fitar a Abuja.