- Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ya bukaci yan Najeriya dasu cigaba da kare kansu daga kamuwa da cutar covid-19, a yayinda sanfarin Delta na cutar ke cigaba da yawaita
- Acewar sa dole ne mu cigaba da gwaje-gwaje domin gano yanayin cutar a Kasar, tare da kula da dukkanin iyakoki na kasar domin hana shigowa da cutar
- Ministan yace Najeriya ta samu rigakafi na Naira Miliyan 40 na Kamfanin J$J domin cigaba da rigakafi a Kasar
Ministan Lafiya Dr. Osagie Ehanire yace cutar Covid-19 sanfarin Delta itace tafi yawa a Kasar, inda ya bukaci Yan Najeriya dasu kula da dukkanin matakan kariya dake garesu, gami da cigaba da yin gwaje-gwaje.
Dayake jawabi a lokacin taron Kwamitin Shugaban Kasa akan cutar Covid-19 a ranar Litinin a Abuja, Ministan yace, “wannan bullowar cutar Covid-19 karo na uku ta tabbata ya kusan tafiya, saboda har yanzu babu wani karuwar cuta da yawan mace-mace.
“Amma ba wayau bane ka dauka cewa cutar ta tafi, musamman yadda ake samun cutar na yin Kasa tana sama, Kuma dole ne a gano wadanda ta kama, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutum 480 A Burkina Faso
“Hujjoji sun bayyana cewa Cutar Corona sanfarin Delta itace tafi kowacce cuta mafi yawa a kasar. Dole ne musanya dukkanin matakan kariya, gami da cigaba da gwaje-gwaje domin gano yanayin da Kasar mu ke fuskanta.
“Akwai rahotannin dake cewa, akwai cutar Covid-19 wani sanfari dake yawo a wasu Kasashen, yanayin da dole ne zamu rika dubawa, domin tabbatar dacewa mun dauki matakan gaggawa.
“Kuma dole zamu zama masu lura a wuraren shigowa kasar mu, ciki harda iyakokin kasa domin magance shigowa da cutar Covid-19 a kasar. An samu wadanda suka kamu da cutar da dama ta hanyar gwaje-gwaje da aka gudanar, gami da kula dasu.
Akan batun maganin rigakafin cutar, Ministan ya bayyana cewa, gwamnati ta samo magani Miliyan 40 na Kamfanin J&J, wanda zai iso nan bada jimawa ba, wanda acewar sa, dukkanin jahohi sun karbi rigakafin Covid-19 na AstraZeneca da Moderna gami da J&J, domin gudanar da rigakafi kashi na biyu dake wakana, a yayinda Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ingancin maganin da Lafiyar sa.