Ballaellen dan takarar gwamnan Jihar Anambra karkashin inuwar jam’iyyar PDP Valentine Ozigbo ya ce har yanzu babu wani dan takara a jam’iyyar tasu da ya wuce shi.
Idan ba a manta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da sunayen yan takara a jihar amma kuma ta cire sunan Ozigbo daga layi.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai taimaka masa Aziza Uko ta fiter, ta ce janye sunansa da hukumar INEC ta yi ya biyo bayan jiran umarnin kotu ne da take yi amma ba wai ko don ba shi ne dan takara ba.
Sanarwar ta ce a yanzu haka tuni PDP ta sanya jami’an da za su tabbatar da cewa komai ya tafi daidai ba tare da wani tsaiko ba.
Comments 1