A ranar Larabar da ta gabata ne dai Ƙungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kwashi kashin ta a hannu gurin Ƙungiyar Chelsea dake kasar Ingila a gasar zakarun nahiyar turai zagaye na biyu.
A wasan farko da kungiyoyin biyu suka yi a makon da ya gabata an tashi ne ci 1:1 a filin wasa na Santiago Bernabeu dake ƙasar Spaniya.
Jimillar kwallayen dai 3:1 kenan hadi da cin kacha da Chelsean ta yi wa Madrid a filin wasa na Stamford Bridge.
Yo sai dai bisa ga dukkan alamu wannan duka da Chelsea ta yi wa Madrid bai ɗaga mata hankali ba kamar yadda aka ga dan wasanta Eden Hazard na Chanchare dariya da yan wasan Chelsea da suka kasance takwarorinsa a baya.
Masana da dama a bangaren wasanni sun bayyana rashin dacewar abin da Hazard ya yi, to amma a bangare guda wasu kuma ba gani ai ba a raba hanta da jini don haka abin da ya yi kara ce.
Ko da yake dan wasan ya nemi afuwar magoya bayansa na Madrid, to amma bisa ga dukkan alamu takaicin nasu bai karw ba domin ko wace rana ka fito babu komai daga gare su sai dai tofin ala-tsine kan dan wasan.
Idan za a iya tunawa dai a kakar bara ne Hazard ya haɗe da Madrid da a wani cefane na gani a faɗa, cefane da ake gani miyar ta gaza yi dandano da ake bukata bayan rashin taɓuka abin arziki sakamakon fama da raunuka da a kullum dan wasan ke yi.