By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya bayyana damuwarsa kan yadda ake kara samun yawaitar marayu a jihar da kuma ‘yan gudun hijira, da sansanonin ‘yan gudun hijira, inda ya dora laifin hakan a kan ayyukan fulani makiyaya.
Ya koka da yadda al’ummar jihar ke barin wasu su dauki nauyin kananan yara marayu da makiyaya dauke da makamai ke rabasu da iyayen su ba tare da wani fatan tsira ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin bikin godiya ga iyalan mai shar’ia Polycarp Kwahar a cocin ECWA, dake Makurdi jiya.
“Abin takaici ne yadda akasarin yaran da ke sansanin ‘yan gudun hijira sun zama marayu saboda Fulani makiyaya da ‘yan ta’adda wadanda suka kashe iyayensu,” in ji Gwamnan.
Sannan ya kuma yi kira ga al’ummar Binuwai da su rungumi wannan kalubale ta hanyar yin kokarin tallafa wa marayun da suka makale a sansanonin ba tare da fatan samun kulawar iyaye ba.
Yayin da yake tunawa da cewa shekaru uku da suka gabata iyalansa sun dauki marayu hudu daga gidan marayu na Mama Abayol dake Makurdi, kuma sun ci gaba da bayar da tallafi ga wannan fanni na yara, gwamnan ya yi kira ga masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen tallafawa ga yaran a jihar.
Ya ce: “Akwai marayu da yawa a sansanonin ‘yan gudun hijira kuma da yawa daga cikinsu basu ma san iyayensu ba saboda ’yan ta’adda Fulani makiyaya sun zo sun kashe su. Kuna iya yin tasiri a rayuwarsu kuma Allah zai saka muku
Gwamnan ya yi godiya ga Allah daya yi wa Misis Nguasen Kwahar lafiya wacce a farkon shekarar ta yi rashin lafiya amma ta hanyar mu’ujiza ta tsira.