Gwamnan jihar Neja, Sani Bello ya bayyana cewa akwai bukatar kafa sansanin sojin ruwa a garin Shagunu, dake karamar hukumar Borgu na jihar a wani mataki na dakile hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Bello, ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Sakatariyar watsa labaran gwamnan, Mary Berje, ta fitar a garin Minna a ranar Asabar, inda ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da shugaban Hafsan Sojin ruwan Vice Admiral Ibok Ekwe-Ina, ya kai masa.
Gwamnan ya kara da cewa sansanin sojin ruwan zai dakile ayyukan ‘yann bindigar da suke shigowa daga makwabtan kasarnan zuwa wadansu jihohin Nijeriya. Sannan har wala yau gwamnan ya ce sansanin sojin ruwan zai taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiki wajen ganin ta bunkasa walwalar al’umma ta hanyar yi musu tituna da kuma samar musu ruwa da wutar lantarki. Inda ya kara da cewa; baya ga samar da tsaro idan aka kafa sansanin sojin ruwan a Shagunu, hakan ma zai bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin mutanen yankin. Kuma ya ce zai kuma zama muhalli na bankado ayyukan bata gari, tunda a cewarsa wuri ne ya hada kasarnan da wadansu kasashen yammacin Afrika.
A na shi jawabin, Ibas ya tabbatar da gwamnan cewa zai duba yiwuwar kafa sansanin sojin ruwan a jihar. Ya jinjinawa gwamnan bisa hankoronsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da yake mulka.