- Hargitsi ya janyo mutuwar mutane biyu da jikkata mutane da dama a Ibadan
- Hargitsin ya janyo mutuwar mutane biyu a Ibadan inda wasu ƙungiya wanda Mr. Munkaila Lamidi ke Jagoranta wadda akafi sani da Auxiliary, sun farmakin wasu masu shaguna dake kan titin Iwo dake Ibandan babban birnin Oyo a ranar Laraba.
- TVCNEWS sun ce Farmakin da aka kaima masu shagunan ya cigaba ne tun bayan sabanin da aka samu tsakanin yaran Auxiliary da ƙungiyar sufurin motoci a ranar Litinin.
KARANTA:-
Ƴan bindiga sun datse kan mai Gadi lokacin da zasu shiga Gidan wani Ɗanmajilisa
Lamarin ya janyo mutuwar mutane biyu daga kowane bangare na Auxiliary da NURTW.
A ranar Laraba ne wasu dake zargi yaran PM dinne sukai dirar mikiya a yankin na Iwo inda ake sayar da wayoyi.
Lamarin ya janyo mutuwar mutum daya daga sashin NURTW, Hakazalika ya sabbaba raunuka ga mutane da damak Waɗan da ke kan hanya masu tafiya da wadanda suke kasa kayansu, wasuma basu tsaya kwashe kayan ba suka zuba a guje don ceto ransu.
A WANI LABARIN: Ana zargin Jami’an ƙasar Myanmar da bankawa wani ƙauye wuta.
Jaridar Aljazeera ta ruwaito cewar ranar talatar da ta gabata ne wani ƙauye me suna Kin Ma, mai kimanin mutane 800 da gidaje 200 aka wayi gari ya koma toka.
Jami’an tsaron sun bankawa kauyen wuta ne bayan gamzawa da mutanen ƙauyen sukayi da abokan aikin su, inda labari ke zuwa lamarin ya janyo mutuwar wasu tsofaffi biyu.
Lamarindai ya janyo zanga-zanga a sassan ƙauyukan da sauran garuruwan dake ƙasar jin kadan bayan labarin aika-aikar da jami’an tsaron sukayi a ƙauyen