Ga wasu Kudirorin sanata Malam Uba Sani Sanatan Dake wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya
12. Kudirin Dokar Hakkin Dan-Adam Ta Kasa (Kwaskwarima) 2020
Kudirin ya kunshi bukatar sauya dokar Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam ta shekara ta 2010, ta yadda matasa da masu fama da kakasa za su samu wakilici, domin tabbatar da ganin an tafi da kowa a matakin tarayya. Shi ma ya tsallake karatu na 1 a zauren majalisar dattawa.
KARANTA:- Nigeria da Kaduna sun yi Babban rashin Basarake, inji Sanata Uba Sani
KUDURIN MALLAM Uba Sani A MAJALISA NA 13
13. Kudirin Dokar Hukumar NDLEA (Kwaskwarima) 2020
An gabatar da wannan Kudiri ne, domin kara wa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa kwarin gwiwar kawo karshen matsalar shaye-shaye da ta addabi musamman yankin arewacin Nijeriya, tare da sa ido a kan yadda ake safarar kwayoyi ko kuma yin su a cikin al’umma. Kudirin shi ma ya tsallake karatu na 1 a zauren majalisar dattawa.
KARANTA:- Tattalin Arzikin mu zai dawo Kuma zai cigaba da bunkasa~Sanata Uba Sani
KUDURIN MALLAM UBA SANI A MAJALISA NA 14
14. Kudirn Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda (2020)
An gabatar da Kudirin ne, da bukatar sauya fasalin dokar Hukumar Kula da Harkokin ‘yan sanda ta shekara ta 2001, zuwa hukumar kulada harkokin ‘yan sanda ta tarayya, wanda za a dora wa alhakin hukunta manyan jami’ai, baya ga shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, a kuma ba ta iko kora ko dakatar da duk wani mai rike da mukami a fannin aikin dan sanda. Shi ma tuni ya tsallake karatu na 1 a zauren majalisar dattawa.
KUDURIN MALLAM Uba Sani A MAJALISA NA 15
15. Kudirin Dokar Aikin Dan Sanda (Kwaskwarima) 2020
Kudirin ya kunshi bukatar sauya fasalin ayyukan ‘yan sanda a jihohi 36 na kasar nan, a kuma sauya sunan hukumar kula da harkokin ‘yan sanda, zuwa hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta tarayya, tare da shawo kan wasu mas’aloli da ke tattare da dokar aikin dan sanda ta shekara ta 2020. Wannan kudirin shi ma ya tsallake karatu na 1 a zauren majalisar Dattawa.
KUDURIN MALLAM Uba Sani A MAJALISA NA 16
16. Kudirin Kafa Dokar ‘Yan Sandan Jihohi (2020)
An gabatar da wannan Kudiri ne, da bukatar samar da hukumar kula da harkokin ‘yan sandan Jihohi, wadda za a ba ikon ladaftar da jami’ai, in banda ainihin ‘yan sandan gwamnatin tarayya, ya kuma kasance ita ke da ikon kora ko dakatar da duk wani jami’in dan sandan jiha, baya ga Kwamishinan ‘Yan Sanda.
Tuni shi ma ya tsallake karatu na 1 a zauren Majalisar Dattawa.
Kawo yanzu dai Tarihi ya nuna cewa Sanatan shine mafi Kai Kudirorin a duk Tarihin sanatocin da Suka wakilci kaduna ta tsakiya a majalisar ta dattijan Nageriya.