Harin Ƴan Ta’adda: Uba Sani ya Tallafi Al’ummar Giwa da Ƙaura da Kayayyakin Jinƙai na Miliyan 10
Sanata Uba Sani ya Kai Kayayyakin Agajin gaggawa na kimanin Niar miliyan Goma 10 ga Al’ummar Ƙaramar Hukumar Giwa da Kaura wanda harin ‘yan ta’adda ya shafa.
Dan takarar Gwamnan jihar kaduna a Ƙarƙashin jam’iyar APC Kuma sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijan Najeriya Sanata Uba Sani ya bayar da kayan agaji ga al’ummar da ta’addancin ƴan bindiga ya shafa a ƙaramar hukumar Giwa.
Haka zalika Sanatan ya bayar da tallafin kayan agaji ga al’ummar da rikicin ya shafa a ƙaramar hukumar Kaura.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Manhajar Wayoyin Hannu Don Tallafawa Harkokin Kiwon Lafiya
A cikin wata wata sanarwa da Babban Jami’in na Sanata Uba akan Kafafen Yaɗa Labaru, kuma shugaban shiyya na mazabu Arc Abubakar Rabiu Abubakar ya fitar.
Kayayyakin da Sanatan ya raba sun haɗa da; Galan-Galan na Man gyaɗa, da Buhunan shinkafa, da katan-katan na Taliyar indomi, da tabarmi da barguna da sauran kayan abinci.
Sanatan ya jajantawa al’ummar da abin ya shafa a waɗannan yankuna, tare da addu’ar Allah ya ba su ikon jure raɗaɗin wadanda suka rasa rayukansu.
Idan dai za a iya tunawa a ƴan kwanakin baya Sanatan ya Kai ƙudiri a zauren majalisar Dattawan, akan matakin da zai bai wa jami’an soji damar gudanar da ayyuka ba tare da tangarda ba, wajen shafe masu aikata laifuka a yankunansu.
Sanatan ya bayyana matukar bakin ciki da takaicin sa dangane da hare-haren da ake kaiwa ƴan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba da dukiyoyinsu.
Tawagar da ta ziyarci karamar hukumar Kaura ta samu jagorancin Engr Namadi Musa wanda tsohon darakta janar na kungiyar addinai ta jihar Kaduna, da tsohon shugaban karamar hukumar kajuru Hon Cafra Caino, da shugaban karamar hukumar Jaba Hon Ben Jock.
Hon Banta Bala Bantex, Hon Donatus Adamu, hon. Joy Akut da Saratu Abdulazeez ma suna cikin tawagar.
Yayin da tawagar da suka ziyarci ƙaramar hukumar Giwa karkashin jagorancin Hon. Bashir Zubairu Birnin Gwari, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna tare da mataimakin shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa Hon Nazir Sunusi, Engr Jamil Ahmad Muhammad, Hon Ibrahim Shehu Haske da Alh Ibrahim Musa Tawagar ta samu kyakkyawar tarba daga shugaban karamar hukumar Giwa, shugabannin al’umma da sauran jami’an jam’iyyar. Tawagar ta ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da aka tanadar domin raba kayayyakin tare da su da jajanta musu bisa wannan abin takaici.
A Karamar Hukumar Kaura, Tawagar ta samu tarbar Majalisar Gargajiya ta Kaura, Wakilin Shugaban Karamar Hukumar Kaura, Kungiyar Cigaban Kaura Kaura Development Association and Kaura IDP Forum)
Sanatan ya raba kayayyakin na kimanin milyan Goma 10m kamar yadda sanarwa ta nuna.