Wani harin bam da aka kai kan masu ibada a masallacin ‘yan Shi’a dakebirnin Kunduz na kasar Afghanistan ya kashe a kalla mutane 50 a yau Juma’a.
Wannan dai shine harin da ake ganin ya fi zubar da jini tun bayan lokacin da sojojin Amurka suka bar kasar.
Mutane da dama da suka jikkata daga ‘yan tsiraru sun ji rauni a fashewar Bam din, wanda haryanzu Babu wata kungiya da ta yi ikirarin Kai harin, amma da alama an tsara shi ne, don kara dagula al’amura a Afghanistan sakamakon karbe ikon kasar da kungiyar Taliban ta yi.
Wata majiya daga Masana kiwon lafiya a Asibitin lardin Kunduz ta ce, an kai mutane 35, da raunata sama da 50 a can, yayin da wani ma’aikacin asibitin, ya ba da rahoton mutuwar mutane 15 da jikkata wasu da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Korona ta kashe mutum biyu a Abuja, Mutane 127 sun kamu a Nigeria
Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fada a bayyana cewa, mutane da dama da ba a san adadinsu ba sun mutu, da jikkata wasu da dama, a “Fashewar da ta faru a cikin masallacin‘ yan uwanmu ‘yan Shi’a a Kunduz” inji shi.
Har kawo hada wannan rahoto Babu wata kungiya da ta yi da’awar kai harin, amma kungiyar IS, babban abokin hamayyar Taliban ce, ta yi ikirarin irin wannan ta’asar a baya-bayan nan.
Mazauna Kunduz, sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP fashewar ta auku ne a masallacin ‘yan Shi’a a lokacin sallar Juma’a, Sallah mafi muhimmanci a cikin mako ga al’umar Musulmai.