Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar sojoji uku a wani hari da wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka kai wa Sojojin Bataliya ta 7 a ranar Lahadi a hanyar Kubwa zuwa Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Yayin da ake samun rahotanni masu cin karo da juna game da hasarar rayuka a harin, mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Brigade, kaftin Godfrey Abakpa, ya ce sojoji uku ne suka mutu a arangamar.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/dan-takarar-gwamnan-jihar-benuwe-rabaran-alia-ya-musanta-zabar-tsohon-minista-a-matsayin-abokin-takararsa/
Ya karyata rahotannin da ke cewa sojoji sunyi batan dabo a yayin da ake gudanar da wannan rahoto.
Haka kuma bai bayyana sunayen sojojin da aka kashe ba amma Jaridar LEADERSHIP ta tattaro cewa wani Kaftin da sojoji biyu sun mutu a harin.
Ya ce, “Babu wani soja da aka sace, sai dai mun samu wadanda suka ji raunuka ne kawai, kuma an kwashe su.”
Rahotannin leken asiri sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun yiwa babban birnin tarayya kawanya ne da nufin kai hari a makarantar koyon aikin lauya da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja da wasu cibiyoyin gwamnati.
Majiyoyin soji sun shaidawa LEADERSHIP cewa harin ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda sun mamaye babban birnin kasar amma hukumomin kasar sun ce suna nan suna bin maharan.
Kyaftin Abakpa ya ce a ranar Litinin din da ta gabata, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi wa dakarun Bataliya ta 7 da ke sintiri a kan hanyar Kubwa zuwa Bwari kwanton bauna.
Ya kara da cewa sojoji uku ne suka jikkata yayin harin kuma an kwashe su zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Ya kara da cewa, “Harin kwanton bauna da ya afku a yankin na Bwari ya nuna cewa a zahiri ‘yan ta’addan suna cikin wurin kuma maiyuwa ne su kai hari a makarantar koyan aikin lauya da ke Bwari kamar yadda aka ruwaito a baya.”
Harin dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da ‘yan ta’addan suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai a wani faifan bidiyo.