Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya amince da cewa jami’an tsaro sun kasa dakile harin da ‘yan ta’adda suka kai a cibiyar gyaran hali ta Kuje da ke Abuja.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 5 ga watan Yuli, 2022, a daidai lokacin da ake kokarin samar da kayan aiki ga jami’an.
KARANTA ANAN: Jaruman Kannywood Sun Rungumi Tafiyar Wata Jam’iyya A Kano
Ministan wanda ke magana a wani zaman binciken da kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai da ke bincike kan harin ya yi, ya ce akwai jami’an tsaro 65 dauke da muggan makamai da suka yi niyyar dakile harin, amma abin ya ci tura.
Ya kara da cewa adadin wadanda suka tsere a yayin harin sun kai mutum 888.
Majalisar ta bayyana damuwarta ne cewa harin ya dauki tsawon sa’o’i ba tare da wani sa hannun jami’an tsaro na zahiri ba don dakile shi.
A wani labarin kuma: Abin Kunya Ne Ace Har Yanzu Najeriya Na Shigo Da Man Fetur— Godwin Obaseki
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana ci gaba da shigo da man fetur a Najeriya, duk da cewa kasar na daya daga cikin manyan kasashe masu arzikin danyen mai a duniya, a matsayin abin kunya.
Obaseki ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a Ewohimi, na karamar hukumar Esan ta kudu maso gabas ta jihar Edo, a wajen taron bikin cika shekaru 10 da nada Chief Jeremiah Ighodalo, mahaifin shugaban bankin Sterling Plc, Dr. Asue Ighodalo hawa kan karagar mulki.