By Abbas Yakubu Yaura
An lalata sansanin ‘yan bindiga da ke kusa da kauyen Kambari a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa harin na sama wanda aka fara tun kwanaki uku da suka gabata, an kai shi ne a sansanonin ‘yan bindiga, inda aka ce an kashe ‘yan bindiga da dama.
DUBA WANNAN LABARIN: 2023: Jam’iyyun Siyasa Da Dama Ne Basu Gabatar Da Rajistar Mambobin Su Ba – INEC
Wakilinmu ya samu labarin cewa an kashe wasu mutane 3 da ke kan babura a kewayen Kwatan Nanido da ke karamar hukumar Gassol a harin da jirgin ya kai.
An kuma tattaro cewa ‘yan bindigar sun shafe watanni biyu suna can a yankin Kambari kuma an ce su ne ke da alhakin yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a kauyuka da dama da ke fadin kananan hukumomin Bali, Gassol da Karim Lamido na jihar.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojin saman Najeriya ya ci tura.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce rundunar ta san da harin, inda ya ce rundunar sojin sama ce kawai.
Comments 1