By Abbas Yakubu Yaura
Sama da mutane 60 ne harin tayar da bama-bamai na ranar Litinin ya rutsa dasu, kamar yadda jigo a jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana.
DUBA WANNAN LABARIN: Rashin Tsaro: Kamfanin Azman Da Air Peace Sun Dakatar Da Zirga-zirga Zuwa Filin Jirgin Sama Na Kaduna
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito yadda ‘yan ta’addan suka tayar da bam a hanyar jirgin kasa tare da bude wuta kan fasinjoji, inda suka yi awon gaba da wasu tare da kashe wasu.
Har yanzu ba a sami adadin wadanda suka mutu a hukumance ba, amma binciken da Jaridar Daily Trust ta samu a ranar Talata ya nuna cewa akalla mutane shida ne suka mutu.
Amma da yake magana a Eko Hotels, Legas, wurin taron Bola Tinubu Colloquium na 13, dan takarar shugaban kasar ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi.
Ya kuma ba da sanarwar soke taron shekara-shekara, karo na farko a tarihinsa.
Tinubu ya ce ya dauki matakin ne domin karrama wadanda suka rasa rayukansu a harin ta’addanci.
“Yanzun an sanar da ni wani lamari mai ban tausayi a kasarmu, abin bakin ciki kwarai da gaske, cewa sama da mutane 60 ne lamarin ya shafa inda wasu da dana aka kashe a harin tayar da bam a cikin jirgin kasa tsakanin Kaduna da Abuja a daren jiya. Wannan lamari ne mai matukar muni game da tsaron rayuka a kasar nan kuma yana bukatar a yi tunani sosai.”
“Don in kasance a nan ina murna, raye-raye da jin daɗin kaina, bai nuna cikakkiyar damuwa ga ɗan jiha da babban ɗan ƙasar nan ba.
“Bai kamata a gudanar da wannan taron ba. Na tuntubi mutanen da kuke gani a kusa da ni a nan kuma sun amince da ni kuma kasancewarsu masu kishin dimokradiyya, na ba da kaina ga shawararsu cewa sun amince a soke wannan taron.”