Daya daga cikin mata masu juna biyu da aka sace daga jirgin kasa a Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022, ta haihu.
Wani dangin wanda abin ya shafa ya bayyana haka a wata hira da ya yi gidan talbijin na ARISE TV.
A cewar gidan talabijin din, makusancin matar ya ce an yi dauko Wani likita a boye zuwa cikin sansanin domin ya kula da haihuwar matar.
Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addar na da tsarin hadin kai saboda yadda suka samu damar kai kayayyakin jinya cikin dajin, al’amarin da suka bayyana a matsayin har yanzu yake baiwa jami’an gwamnati da na tsaro mamaki.
“Matar da aka ruwaito tana dauke da ciki wata takwas a lokacin da aka kai harin, ta haihu lafiya bayan da aka ce ‘yan ta’addan sun gayyaci jami’an lafiya domin zuwa wurinta. Sai dai ba a san halin lafiyar jaririn ba.”
“A cewar rahotanni daga majiyoyin ‘yan uwan matar, ta haihu ne da taimakon likitocin da ‘yan ta’addan suka kawo. Za mu kuma iya ba da rahoton cewa, ‘yan ta’addar na neman a sako manyan kwamandojinsu domin musanya da fasinjojin jirgin da aka sace,” in ji ARISE a cikin rahotonta.
Iyalan wadanda aka yi garkuwa da su sun roki gwamnati da ta gaggauta shiga tsakani domin sakin su, amma ‘yan ta’addan sun bukaci a musanya su da kwamandojin su da ke tsare a halin yanzu.
A farkon makon nan ne ‘yan ta’addan suka fitar da hotunan wadanda aka yi garkuwa da su.
Daga cikin wadanda aka gani akwai ma’aurata tare da ‘ya’yansu hudu, tsofaffi mata biyu da maza 17.
KiAkalla mutane tara ne suka mutu bayan da ‘yan ta’addar suka tayar da bama-bamai kan titin jirgin tare da bude wuta kan fasinjojin.
A Wani labarin Kuma na daban.
Akalla kwamishinoni 11 ne suka yi murabus daga mukamansu a majalisar Kwamishinin Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinonin sun hada da na ma’aikatun Fili da gidaje, Aminu Bala Bodinga,; Matasa da Wasanni, Bashir Gorau; Kudi, Abdussamad Dasuki; harkokin tsaro da hukumomin su, Garba Moyi da Kwamishinan Ma’aikatar harkokin addini na jihar ta Sokoto, Abdullahi Maigwandu.
Sauran sun hada da kwamishinonin ayyuka, Salihu Maidaji; Ma’adanai, Abubakar Maikudi; Albarkatun Ruwa, Shu’aibu Gwanda Gobir; Muhalli, Sagir Bafarawa da karamar hukumar, Manir Dan’iya wanda har yanzu mataimakin gwamnan jihar ne da kuma kwamishinan kasuwanci, Bashir Gidado.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ci gaba da cewa Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato Sa’idu Umar Ubandoma da Shugaban Ma’aikatan Gwamnan Jihar Mukhtar Umar Magori su ma sun yi murabus.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa Tambuwal ya amince da murabus din nasu.
A cikin makonni biyun da suka gabata, kusan kwamishinoni 50 ne suka yi murabus a jihohi daban-daban Dake fadin kasar nansaboda zaben shekarar 2023.
Sashe na 84 (12) na dokar zabe ta shekarar 2022 (kamar yadda aka gyara) ya nuna cewa, Babu Wani Dan Takarar da zai tsaya takarar kujerar siyasa ta zabe a zaben shekarar 2023, Kuma Yana rike da mukamin siyasa na nadi.
Bisa jadawalin zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fitar, jam’iyyun siyasa na da damar gabatar da sunayen Yan takaransu a babban zaben kasarnan zuwa ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2022.