An jiyo karar fashewar wani mummunan abu a wani masallaci dake Kabul babban birnin kasar Afganistan, in ji ‘yan sandan kasar.
Ana kyautata zaton fashewar ta auku ne yayin sallar magariba, inda ta kashe akalla mutane uku tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda kungiyar agajin gaggawa ta NGO ta bayyana.
Kafar yada labaran kasar ta nakalto Khalid Zadran, kakakin rundunar ‘yan sandan Taliban na birnin Kabul na cewa an samu fashewar wani abu a arewa maso yammacin birnin.
Rahotanni sun ce limamin masallacin Siddiqi na cikin wadanda suka mutu.
Jami’an Soji Sun Kama Mutum 7 Da Ake Zargin Masu Garkuwa Ne A Kaduna
Ba a dai san ko su waye suka kai harin ba, wanda ke zuwa mako guda bayan da aka kashe wani fitaccen malamin nan mai goyon bayan Taliban a wani harin kunar bakin wake da aka kai, shi ma a Kabul. Sai dai daga bisani Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin daga a baya.
Kungiyar agajin gaggawa ta Italiya – wacce ke aiki a Kabul – ta ce ya zuwa yanzu an sami gawarwakjn mutane uku.
Kungiyar mai zaman kanta ta kuma wallafa a shafinta na Twitter cewa ta karbi mutane 27 da suka jikkata sanadiyar fashewar, ciki har da yara,” in ji ta.
Wani jami’in leken asirin Taliban ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa mutane kusan 35 ne suka samu raunuka ko kuma suka mutu, kuma adadin na iya karuwa a kowani lokaci.
Shaidu sun bayyana jin karar fashewar wani abu mai karfi wanda ya farfasa tagogi a gine-ginen da ke kusa da masallacin.
Jami’in wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce fashewar ta faru ne a wani masallaci kan masu ibada a yankin Khair Khana na birnin Kabul.
“Tawagar leken asirin sun kasance a wurin da fashewar ta auku kuma ana ci gaba da gudanar da bincike”, in ji shi.
Kakakin kungiyar Taliban ya ce sun yi Allah wadai da wannan mummunan harin.