By Abbas Yakubu Yaura
Dan majalisar wakilai daga jihar Filato, Hon. Yusuf Gagdi na Jam’iyyar APC ya yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta samar da dokokin da za su bai wa ‘yan kasar damar rike makamai domin kare kawunan su.
Ya ce halasta daukar makamai zai taimaka matuka wajen magance yawaitar hare-hare da kashe-kashe a cikin al’umma.
Gagdi ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, jim kadan bayan ya ziyarci wasu al’ummomi a kananan hukumomin Kanam da Wase da ‘yan bindiga suka kai wa hari.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito idan za’a iya tunawa cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun afka cikin wasu al’umma a karamar hukumar Kanam da Wase; inda suka kashe mutane sama da 100, tare da jikkata da dama da kuma kona gidaje da dama.
Gagdi wanda ke wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar tarayya ya ce dole ne a samar da tsauraran matakai don daidaita amfani da makamai da ‘yan kasar ke yi.
“Idan muna son dakile yawaitar hare-hare a cikin al’umma, ya kamata mu samar da dokokin da za su bai wa ‘yan kasa damar rike makamai.
“Alal misali, wadanda suka kai wa jama’ata hari sun san cewa ‘yan yankin su ma suna da makamai, ba za su zo ba, kuma ko sun yi, asarar ba za ta kai haka ba.
“Amma dole ne a samar da tsari kan amfani da makamai; duk wanda ya yi amfani da shi ba daidai ba to a daure shi ko ma a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Amma ina gaya muku, idan aka bar ‘yan kasa su rike makamai domin kare kansu, duk wadannan hare-hare da kashe-kashe za su kawo karshe,” inji shi.
Gagdi ya yi kira ga jami’an tsaro da su rika aiki da rahotannin sirri a kodayaushe domin kaucewa aukuwar lamarin da ka iya haifar da tabarbarewar tsaro.
Ya ci gaba da cewa za a iya kaucewa hare-haren da ake kai wa mazabarsa idan har jami’an tsaro suka yi aiki da rahoton leken asirin da suke da shi.
Sai dai dan majalisar ya yabawa rundunar sojin da suka yi gaggawar kai dauki tare da tura jami’ai zuwa yankunan da lamarin ya shafa.
Comments 1