Wasu da ake kyautata zaton fulani makiyaya ne sun yi wa mutum takwas ‘yan uwa kwanton bauna tare da kashe wasu mutane biyu a Danda Chugwi da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Shaidu sun ce an kai wannan mummunan harin ne cikin dare ranar Lahadin nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Rwang Tengwog, sakataren kungiyar Berom Youth Mooulders (BYM), shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels da ke Jos.
KARANTA WANNAN https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-kungiyar-asuu-ta-tsawaita-yajin-aikin-da-ta-keyi/
Tengwog ya ce maharan sun shiga harabar ne da misalin karfe 9 na daren Lahadin nan inda suka fara harbe-harbe kai tsaye wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane takwas.
A cewarsa, mutane biyun da suka jikkata, sun samu raunukan harbin bindiga kuma an kai su asibitin Vom Christian domin kula da lafiyarsu cikin gaggawa.
Sakataren BYM ya jaddada cewa, kamar yadda a daren jiya, an harbe mutane bakwai na iyalan Pam Gyang, sannan kuma na takwas da aka kashe ya mutu da sanyin safiyar nan.
Wadanda aka kashe sun hada da manya uku da yara biyar, wadanda har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana gab da binne su.
Mazauna yankin sun ce akwai yuwuwar an kashe wasu karin mutanen, sai dai har yanzu ‘yan sanda da kuma jami’an tsaro na musamman masu tabbatar da doka da oda a jihar, ba su tabbatar da faruwar harin ba, kuma har yanzu ba a san abin da ‘yan bindigar suka kayi ba.