By Abbas Yakubu Yaura
Mazauna karamar hukumar Sabon Birni dake jihar Sokoto sun koka kan ikirari da rundunar ‘yan sanda suka yi kan adadin wadanda aka kashe a harin baya-bayan nan da aka kai kauyukansu.
Rundunar ‘yan sandan jihar, yayin da take tabbatar da faruwar harin, tace wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari a kauyuka uku da ke yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sanusi, ya bayyana cewa an kashe mutane tara a hare-haren da aka kai a ranakun 15, 16 da 17 ga watan Nuwamba na shekarar 2021.Wannan shi ya kawo adadin mutanen da ‘yan bindiga suka ce an kashe zuwa 52 a cikin sa’o’i 72 a gabashin jihar.
Idan za a tunawa jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar Litinin ne gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, ya tabbatar da kashe mutane 15 da 12 a Ilella da uku a Goronyo, a wani harin da aka kai da sanyin safiya ranar, Sai dai a ziyarar da gwamnan ya kai garin Ilella a ranar Laraba da yamma, adadin wadanda suka mutu ya haura 43.
Ko da yake Sanusi yana rike da adadi a kan hare-haren Illela da Goronyo, ya tabbatar da harin na kwanaki uku a Sabon Birni, cibiyar ‘yan fashi a jihar.Sanusi yace, “Harin farko da aka kai a Garin Zago a karamar hukumar Sabon Birni, ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da yin garkuwa da wasu uku.
Sannan“A wani harin da aka kai a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2021, an kai wa wata mota hari a kauyen Gaji, amma ba a samu asarar rai ba. Harin na uku ya faru ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2021, a kauyen Sangirawa inda maharan suka kashe mutane shida tare da jikkata wasu da dama.”
A halin da ake ciki, wani tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Idris Gobir, ya caccaki wannan adadi da ‘yan sanda suka bayar.Gobir wanda yanzu haka mataimaki na musamman ne ga Ministan ‘yan sanda Maigari Dingyadi ya shaida wa wakilinmu cewa adadin wadanda suka mutu a harin sun kai 27.
Kazalika yace yayin da aka kashe mutane 21 a ranar 16 ga watan Nuwamba a kauyuka uku, an kashe hudu a ranar 15 ga watan Nuwamba, yayin da wasu shida suka jikkata, inda wasu biyu kuma aka kashe a ranar 14 ga watan Nuwamba.Gobir ya ci gaba da cewa ya na da sunayen dukkan mutanen da aka kashe da kuma wadanda suka jikkata a harin.