• Yan bindiga sunyi sanadiyar, mutuwar Yan sanda 13 a Zamfara, da wasu Mutum 3.
• Sun yi sunkurin Kai hari ne a awani yanki da ke kusa kudancin farin Gusau, sai jami’an soji su ka dakile yunkirin su.
• wani mazaunin garin da lamarin ya afku na Korar Mota ya ce, ya ga gawar-wakin uansanda Sha uku.
Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda 13 da kuma wasu Mutum uku, a wani hari da su ka kai a yankin Kurar Mota, dake karamar hukumar Bundugu na jihar Zamfara.
A cewar mazauna yankin sun ce, yan bindigan sunyi yunkurin farmakan yankin Magami ne, dake da nisan kilomita 50 gada Kudancin Gusau babban birnin jihar, sai jami’an soji suka dakile yunkirin nasu.
” Sun janye yunkurin su ne, bayan jami’an soji sun dakile yunkirin na su, daga nan ne suka nufi wani yanki dake kan hanyar Magami-Dankurmi zuwa Dangulbi inda a nan ne, su ka kashe Mutum guda da kuma fasa shaguna hudu” inji wani mazaunin garin.
“Bayan nan kuma su ka farmaki yankin Kurar Mota, inda suka kai wa jami’an yan sanda dake kusa da wani dakin Shan Magani hari, daga bisani kuma su ka famtsama cikin daji.” Inji shi.
“Jami’an da aka kashe da kuma wadanda suka sami raunuka an kai su cikin garin Gusau a Motocin rundunar yan sanda, kuma nan ne naga gawar-wakin goma sha uku na jami’an yan sanda, sai dai gada bisani, na ga Motocin jami’an yan sanda dama sun nufi inda lamarin ya afku.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mun gano wanda ke son rugujewar jam’iyyar APC, cewar Abubakar Yari
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta Zamfara SP Muhammad Shehu, ya yi alkawarin yi wa wakilin mu karin bayani da zaran ya kammala tattara bayanai, kan rahoton kai harin.
Comments 2