Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Tsohon Jarumi a Masana’antar Kannywwod Kuma Furodusa daya Dade a na damawa da shi a cikin harkar fim Isah A Isah, ya bayyana halin da Masarautar ta shiga a yanzu na rashin tsari da Kuma rashin girmama na gaba.
Jarumin ya bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya in da ya bayyana cewa.
“A gaskiya sanin da na yi wa harkar fim a baya akwai biyayya da girmama na gaba, yadda idan Kai Furodusa ne ana yi maka ladabi haka ma Darakta da sauran manya a harkar fim, Sai ya zama a yanzu an samu sauyi tsarin.”
Ya Kara da cewa “, Daga yaro ya samu wani abu, sai ya rinka garman Kai, haka ma su Matan kowacce tana ji da kanta ta yadda bata ganin girman kowa wannan shi ne yasa aka samu Kai a cikin halin da a ke ciki a yanzu.”
Sannan ya Kara da cewar “Amma da shugabannin Masarautar za su yi abin da ya dace na Shugabanci, to da an magance wannan matsalar Amma dai su ma ba sa yin abin daya dace sai wani abu daban Kuma Hakan ba zai kawo gyara a Masana’antar ba.”
Daga karshe ya yi Kira ga abokan sana’ar dasu hada Kan su domin kawo gyara a cikin Masana’antar shirya finafinai ta kannywwod.