Daga Mukhtar Yakubu Kano.
Duk da cewar harkar fim ba ta tafiya saboda Mutuwar da kasuwar ta yi, to ni tauraruwa ta ba ta fadi ba, domin har yanzu ina nan ina ci gaba da harkokin da na saba yi a baya.
Wannan Kalaman sun fito ne daga bakin fitaccen jarumin Barkwanci Aminu Ali Baba kofar Nassarawa, wanda aka fi sani da Aminu Baba Ari, a lokacin da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Dimokuradiyya dangane da rashin ganin sa, a harkar fim a wannan lokacin.
Jarumin ya ce gaba da cewar, “A yanzu harkar ta koma online, ko kuma fina-finai masu dogon zango, to a baya na bude shafi na na YouTube, ina saka gajerun fina-finan Barkwanci, amma sai na tattara na watsar, amma dai su masu shafukan YouTube din, suna kira na ina yi musu aiki suna biyana, amma dai na yi na saka a shafina, to wannan ba na yi, don haka ina yin talluka ne, na kamfanoni da harkar siyasa, don ka ga tun da harkar ta zama haka, to ba za a zauna ba, don na koma wani bangaren duk da dai da sunan fim din na ke gudanar da sana’ar tawa, don haka ina nan ana damawa da ni.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje ya zama tauraron siyasar Arewacin Nigeria
Da ya juya ga abin da ya ke ci masa tuwo a karya kuwa, a cikin harkar fim cewa ya yi, “Babu abin da ya fi bata mini rai, kamar yadda wani yaro ya ke yin amfani da suna na, da kuma shiga irin tawa ya ke bata al’adar mu ta Hausa, da kuma addinin mu, kuma wasu suna ganin kamar ni na ke yi. To Amma dai Alhamdulillah, yanzu wasu sun fara gane wa, domin na samu labarin kwanakinnan ya je Bauchi, amma da aka gane ba ni ba ne sai aka ki zuwa wajen wasan na sa, to wannan abin yana bata mini rai sosai” a cewar shi.
Comments 1