• Kudin da mutun ya kashe a fim basa da wuwa, sai mutun ya yi sa’a.
• Kafafen talbijin din da suke haske fim bawani kudi suke iya biya ba
• Tun bayar mutuwar harkar CD shikenan aka rage cin moriyar harkar film.
Daga Mukhtar Yakubu Kano
An bayyana harkar fim da wata harkar da ta yi mutuwar da a yanzu babu wani, da ya Isa ya zuba kudin sa, kudin ya dawo a kan lokaci, kamar yadda a ake yin harkar a baya.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Fitacciyar Furodusa, kuma jaruma Hannatu Bashir, wacce aka fi sani da Hanan, a lokacin da su ke tattaunawa da wakilin mu, a kan matsayin da harkar take ciki a yanzu.
Hannatu Bashir wadda za a iya kiran ta da sunan Kallabi tsakanin Rawuna, a cikin masana’antar, domin kuwa ita kadai ce, ta rage a cikin Furodusoshi mata da a ke damawa da ita, duk da yadda harkar ta zamo a yanzu.
Ta bayyana cewar “A yanzu harkar fim ba abu ne da ya ke da sauki ba, saboda yanayin tsadar rayuwa komai ya yi tsada, sannan kuma babu kasuwar don tun da kasuwar C D ta mutu, ya zama sai manyan Gidajen Talbijin, sai ya zama harkar ta tsaya, domin ko sakon mu ma ba ya Isa ga Jama’a kamar yadda ya ke a baya, saboda su gidajen Talbijin din ba sa sayen kayan da zai wadaci masu kallo, domin wanda aka kai musu ma da ya ke hannun su, sai su dauki tsawon lokaci ba su biya ba, don haka a yanzu dai ana yi fim ne kawai, saboda haka idan mun fim matakin farko za mu kai shi Cinima ne a matsayin talla, dan abin da ya samu karbiwa,” inji ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnonin APC sun ta Mai Mala Buni murnar sake zaban shi Shugaban kwamitin jam’iyar
“Idan ka yi sa’a aka karba za a nuna shi a gidan Talbijin, in ka yi sa’a ka mayar da kudin da ka kashe toh!!!, amma fa abu ne mai wuya, don haka ana dai yin harkar ne a yanzu. ”
Ko da mu ka tambaye ta, ko me ya sa suke zuba kudi a harkar da yanzu sun san ta mutu?
Sai ta ce” duk da ta mutu din idan ka yi sa’a kudin ka za su dawo har ma ka samu wani abu, sai dai abin yana da wahala dawowar kudin, domin ka ga ko a yanzu ma na gama aikin sabon fim din da na yi mai suna Shaheeda, wanda za a haska shi a Cinima ta Shoprate da ke Kano, kuma za a fara haska shi a ranar 2 ga watan Yuli Juma’a mai zuwa, don haka ba za mu karaya ba, sai dai fatan Allah ya farfado mana da harkar fiye da yadda ta ke a baya. ”
A karshe Hannatu Bashir ta yi wa masoyan ta fatan alheri dangane da kaunar da su ke nuna mata, a matsayin ta na jaruma kuma Furodusa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood.
Comments 2