Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
A daidai lokacin da harkokin siyasa su ke shirin kankama wadanda su ma yan fim suna cikin mutanen da a ke damawa da su a fagen, su ma a yanzu sun ce, an Sha su sun warke, don haka ba za su yarda a mayar da su gugar Yasa ba.
Daya daga cikin jarumai da su ke jagorantar yan fim da su ke harkar siyasa, T, Y Shaba ne ya bayyana hakan, a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya a kan harkar siyasar yan fim.
Ya Kara da cewar ” a baya yan fim sun bayar da gudummawar su wajen samar da shugabanni a Fagen siyasa a cikin Jam’iyyan nan da mu ke da su, amma da aka gama sai aka mayar da su gugar Yasa ba a ma san da zaman su ba don haka nan gaba an Sha mu mun warke ba za mu kara yarda da hakan ba. “Inji shi
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kai hari Ofisoshin Yan sanda 2 a Shinkafi, Sun Debi makamai
Da muka tambaye shi ko wanne irin matakin yan fim za su dauka nan gaba, sai ya ce:
” A yanzu muna da manufar mu a tsare mun rubuta wacce manufa ce ta ci gaban masana’antar fim duk wanda ya nemi tafiya da mu sai mun ba shi ya gani irin abubuwan da mu ke son a samar mana wanda zai kawo ingantuwar masana’antar mu idan ya yarda sai mu tafi da shi, haka za mu yi a matakin jihar Kano da kuma kasa baki daya” a cewar Shaba.
.
Mun tambaye shi ko akwai Wanda su ke ganin zai yarda da wannan manufar ta su?
Sai ya ce “muna nan dai muna lalune, Amma dai a mataki na jihar Kano, a yanzu wanda muka fara tafiya da shi kuma za mu gabatar masa da tsarin mu, shi ne Abdulkarim A A Zaura don shi muka yarda da tafiyar sa a yanzu, sai kuma nan gaba mu ga abin da zai biyo baya.”
Daga karshe ya yi kira ga ‘Yan fim da su guji yin siyasa babu manufa a nan gaba, domin hakan ce ta sa a yanzu ba a ganin’ yan fim da kima a harkar siyasa.