By Abbas Yakubu Yaura
Wani matashi dan shekara 24 ya mutu sakamakon harbin da wani dan banga yayi a unguwar Oraifite, Enekwasimpu Obosi dake karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.
Marigayin, wanda aka ce dan dangin wanda yayi harbin ne ya gamu da ajalinsa a lokacin da yake rabawa wasu ’yan banga ruwan sha a wajen wani taron daurin auren gargajiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wani ganau wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace angon ya roki marigayin daya taimaka masa wajen hada masa ruwan sha a lokacin bikin sabuwar matarsa.
“Yana tsaka da yin hidimar wasu ‘yan banga ne a gidan abincin mahaifiyarsa, sai daya daga cikin su ya tashi yayi harbi sama kuma harsashi ya dawo kan yaron.
Sai dai “Yaron ya fadi kwatsam, inda nan take jami’an ’yan banga suka garzaya da shi asibiti tare da mutumin daya harbe shi da sauran masu goyon bayansa, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Mahaifiyar marigayiyin ‘yar asalin garin Nri dake karamar hukumar Njikoka ta jihar, an ce ba ta nan a lokacin da lamarin ya faru, sai dai masu tausaya wa wadanda abin ya faru sun yi kokarin dukan wanda ya aikata laifin.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, PPRO, Tochukwu Ikenga, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin tuntubar jami’in dan sanda mai kula da yankin Mista Ekuri Remigius domin tabbatar da hakan.