Hadadiyar Daular larabawa tace, kasuwar mai ta duniya ta na bukatar man kasar Rasha kuma babu wata kasar da ke fitar da man da ka iya maye gurbin kasar ta Rasha a wurin harkar Mai.
Ministan makamashi na kasar Suhal al-Mazrouei ne ya bayyana hakan a yau litinin.
Ministan ya ce yakamta kungiyar OPEC ta zama dunkulaliya, kuma yayi gargadi cewa kada kungiyar OPEC ta bari siyasa ta yi tasiri wurin lalata hadin kan Mambobinta.
Ministan yayi wannan jawabi ne a dai lokacin da aka bayyana cewa masu shiga tsakani za su fara wata tattunawa zaman lafiya tsakanin yau a Istanbul kamar yadda wasu mahukunta a kasar ta Turkiya suka bayyana duk da ba suyi karin bayani ba.
To sai dai rahotonni sun bayyana cewa Shugaba Turkiya Tayyib Erdogan ya tattauna da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho, inda suka amince da kasar ta Turkiya ta jagoranci taron tattaunawar, da ake fatan samun nasara.