Hatsari Ya Hallaka Mutane 30, Yayi Sanadin Ƙonewar Motoci A Kaduna.
Kimanin Mutane 30 suka mutu a wani Hatsarin mota da ya faru akan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru da misalin Karfe 5:30 na yamma kusa da Hawan Mai Mashi a karamar Hukumar Makarfi dake Jahar Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na Ki Amincewa Da Tinubu A 2007 A Matsayin Takarar Musulmi Da Musulmi — Atiku
Mataimakin Shugaban Hukumar Mai kula da kiyaye Hadurra ta kasa reshen Shiyyar Zaria, Abdurrahaman Yakasai, ya tabbatarwa Daily Trust da faruwar lamarin .
Ya bayyana cewa, Haɗari ya rutsa da motoci biyu masu cin fasijojin 18 na motar Toyota tare da ƙirar Volkswagen Gulf, ya Kara da cewa Hatsarin ya faru sanadiyyar mugun gudu da mummunan daukar hannu da motocin ke yi.
Ya bayyana cewa, ” waɗanda suka ji raunuka an hanzar ta Kai su Asibitin Koyar wa na Shika dake Zaria, yayin da aka Kai matattun wurin Adana gawa ta asibitin.”
Kwamandan yace FRSC har yanzu bata gano cewa Lambobin motocin domin tuni an ƙone su.
Amma yace ana ƙoƙari domin gano bayanan waɗanda lamarin ya rutsa dasu.