Dagwa ya bayyanawa manema labarai hakan ne a ranar Talata a garin Minna, inda ya ce hatsarin sun auku ne a tsakanin watan Janairu zuwa watan Satumban 2019.
Cikin wata tara, mutum 266 ne suka rasa rayukansu a sakamakon hatsura 365 akan tituna da ya auku a jihar Neja, kamar yadda Joel Dagwa, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa wato FRSC reshen Arewa ta tsakiya ya tabbatar.
A cewarsa, hatsarin ya shafin mutum 2,097 ne, inda cikinsu mutum 1,303 suka samu raunuka daban-daban.
Kwamandan yankin, ya alakanta hatsarukan da aka samu da gudun wuce kima, da tukin ganganci, tare da kuma daukar mutane na wuce ka’ida, inda ya gargadi direbobi da su guji aikata wadannan dabi’u.
A karshr ya shawarci direbobi da su rika bin ka’idar tuki bisa doron hankali, tare da girmama sauran masu amfani da titunan, inda ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka kama da karya ka’idar tuki.