By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan bisa rasuwar ma’aikatan sa guda biyu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.
DUBA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Koka Kan Rashin Ƙididdigar Gaskiyar Kuɗaɗe A Najeriya, Yayi Kira Da’a Gyara
Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bi sahun ‘yan kasar wajen addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Shugaba Buhari ya bukaci iyalansu da su kalli rasuwarsu a matsayin sadaukarwa ga kasa.
Shugaban wanda ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya sa Shugaba Jonathan ya tsira daga hatsarin, ya bukace shi da kada ya shagaltu da tafiye-tafiyen da yake yi a cikin gida da waje da ya shafi samar da zaman lafiya a gida da wajen kasar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito yadda ayarin motocin Jonathan suka yi hatsari a kusa da filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaban kungiyar matasan kabilar Ijaw na kasa, Peter Timothy Igbifa, ya yi zargin cewa hatsarin wani shiri ne da wasu makarkashiya suka shirya don kawo karshen rayuwar tsohon shugaban kasar gabanin gudanar da babban zabe na 2023.
A cewarsa, ‘yan sandan sun yi amfani da kansu ne a matsayin garkuwar dan Adam wajen kare Jonathan kuma a cikin haka ne suka biya farashi mai tsoka.
Ya yi barazanar cewa matasan Neja-Delta za su durkusar da tattalin arzikin kasar idan wani sharri ya samu Jonathan.
Sai dai hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta shaidawa manema labarai cewa “gudun wuce sa’a” ne ya haddasa hadarin.
Kwamandan hukumar dake kula da reshen babban birnin tarayya Abuja, Samuel Ogar Ochi, ya ce an fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya ce, “A gare ni a matsayina na kwamandan hukumar FRSC na FCT, na samu labarin afkuwar hadarin inda na zarce zuwa asibitin kasa domin tabbatar da halin da wadanda abin ya shafa suke.
“Kuma daga abin da muka tattara shi ne cewa abin hawa na iya kasancewa cikin sauri. Yana tafiya da wani irin gudu ne ya sa direban ya rasa iko. Hoton da muke da shi kenan, amma sai bayan an kammala bincike za a bayyana cikakken bayanin hadarin.”