By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun sauran shugabannin duniya wajen jajantawa rasuwar babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Indiya, Gen Bipin Rawat, da matarsa, da wasu mutane 11 da suka mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.
Shugaba Buhari, a cikin sakon daya aikewa firaministan Indiya, Narendra Modi a ranar Alhamis, ya bayyana mutuwar sa a matsayin asarar da ba za a iya misaltawa ba ga sojojin Indiya da kuma al’ummar kasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu, ya fitar a Abuja, ya ruwaito shugaban Najeriya na cewa marigayi babban hafsan hafsoshin tsaron kasar ya yaba da yadda ake yiwa sojojin Indiya garambawul da jami’an tsaro.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaba Buhari yace “A madadin kaina, gwamnati da al’ummar Najeriya, ina mika sakon ta’aziyyarmu, ga iyalan Rawat,da sauran iyalan mamatan da kuma sojojin Indiya da kasa baki daya yayin da kuke juyayin babban rashin hafsan hafsoshin tsaron kasar, da matarsa. da kuma wasu manyan hafsoshi 11,” in ji shugaban.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa Rawat shi ne babban hafsan hafsoshin tsaron Indiya na farko, matsayin da gwamnati ta kafa a shekarar 2019, kuma ana ganin yana kusa da Firaminista Modi.
Mutumin mai shekaru 63 a duniya yana tafiya ne tare da matarsa da wasu manyan jami’ai a cikin jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Mi-17 na kasar Rasha, wanda ya fado kusa da inda ya nufa a kudancin jihar Tamil Nadu.
Modi yace Rawat fitaccen soja ne kuma “dan kishin kasa na gaskiya” wanda ya taimaka a zamanantar da sojojin kasar.