By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta gaggauta fara cigaba da aikin ceto sauran wadanda suka nutse a kogin Zumba-Guni a lokacin da suke kokarin tserewa daga hare-haren ‘yan bindiga.
DUBA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Daya,Tare Da Bankwa Sakatariyar Karamar Hukuma Wuta A Anambra
Gwamnan ya kuma umurci hukumar da ta bayar da tallafi ga sauran mutanen kauyen da suka gudu.
Wani mazaunin yankin Michael Madaki ya shaida wa wakilinmu cewa an ceto gawarwakin yara hudu da mata tara yayin da ake ci gaba da neman sauran gawarwakin.
Gwamnan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun babbar sakatariyar yada labaran sa, Mary Noel-Berje, ta bayyana lamarin a matsayin abin damuwa da raɗaɗi.
Sannan ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da daukacin al’ummar karamar hukumar Munya.
Ya kuma yi tir da yadda ake ci gaba da kai hare-haren ba gaira ba dalili a kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a wasu al’ummomin jihar.
Gwamnan ya ce duk yadda ’yan ta’addan suka ci gaba da gudanar da ayyukansu na ta’addanci, gwamnati za ta tsaya tsayin daka kuma ba za ta daina kokarin kawo karshen miyagun laifuka a jihar ba.
Da yake yabawa da kokari da sadaukarwar da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka yi, Gwamna Sani Bello ya umarce su da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu.