By Ishaq Dabai
Babu wanda ya tsira bayan da jirgin da ke dauke da fasinjoji 28 ya yin da yayi hatsari a gabashin kasar Rasha a ranar Talata, kamar yadda kamfanonin dillancin labarai na Rasha suka rawaito daga jami’an ceto.
Jirgin Antonov An-26 turbin turboprop yana kan hanyarsa daga babban birnin yankin Petropavlovsk Kamchatsky zuwa Palana, wani kauye dake arewacin tsibirin Kamchatka, lokacin da ya rasa hulda da masu kula da zirga zirgar jiragen sama, in ji ma’aikatar bada agajin gaggawa.majiyar ta Interfax ta ruwaito cewa ana tunanin jirgin ya fada cikin wani dutse ne a lokacin da yake shirin sauka a cikin rashin kyawun yanayi.
Hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasar Rasha ta tabbatar da cewa an gano inda jirgin ya fadi bayan da ma’aikatar agajin gaggawa ta aike da jirgi mai saukar ungulu sannan ta tura tawagogi kasa don neman jirgin da ya bace.
Akwai fasinjoji 22 da ma’aikata shida a cikin jirgin, in ji ma’aikatar.Olga Mokhireva, magajin garin Palana na cikin fasinjojin, hukumar TASS ta rawaito cewa hukumomin yankin suna cewa.Yanayin yankin ya kasance bashi da kyau inda hadari ne lokacin da jirgin ya bace, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rasha ya ruwaito.TASS ta ce jirgin da abin ya shafa yana aiki tun shekarar 1982.
Ka’idojin tsaron jiragen sama na Rasha sun inganta a cikin ‘yan shekarun nan amma hadurra da wadanda suka shafi tsofaffin jirage a yankuna masu nisa, ba sabon abu bane.
Nau’in jirgin sama na zamanin Soviet, wanda har yanzu ana amfani da shi don safarar sojoji da fararen hula a wasu ƙasashe, ya shiga cikin munanan hadarurruka tun lokacin da ya fara aiki kusan shekaru 50 da suka gabata.
Wani jirgin sama mai suna Antonov-28, ya yi karo a dajin Kamchatka a shekarar 2012 a hadarin da ya kashe mutane 10 a kan hanya guda.Masu binciken sun ce dukkan matukan jirgin sun bugu a lokacin hadarin.