Mutane 13 da har yanzu ba a gansu ba kwanaki, bayan wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya afku a garin Bagwai na jihar Kano duk an samu nasarar ceto gawar-wakin su.
An gano dukkan mutane 13 da suka mutu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen zuwa 42.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa jirgin mai dauke da fasinjoji 49 ya kife ne a lokacin da yake jigilar fasinjoji wadanda galibi daliban makarantar Madinatu Islamiyya ne, daga kauyen Badau da ke kan hanyarsu ta zuwa Bagwai domin halartar bikin Mauludi na Annabi Muhammad (SAW).
A baya dai an samu mutuwar mutane 29 a yayin da aka ceto mutane bakwai da ransu.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin, tare da samar da motocin bas guda biyu da za su taimaka wajen jigilar fasinjojin da ke tafiya tsakanin kauyen Badau da Bagwai.
Hakazalika, gwamnati ta raba wa iyalan mamatan kayan agajin da suka hada da buhu 120 na shinkafa, masara, Buhu 60 na sukari da gishiri da kuma tallafin kudi na Naira miliyan 6.