Rahotanni sun ce mutane 5 ne suka mutu yayin da aka ceto wasu hudu daga wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Gwaram da ke jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a kauyen Martaba a lokacin da fasinjojin ke komawa gida bayan kammala sallar Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da wani kwalekwalen da ke dauke da fasinjoji tara ya kife a hanyarsu ta komawa kauyen Martaba bayan sun kammala sallar Juma’a a kauyen da ke makwabtaka da su.
Adam ya bayyana cewa da samun labarin, tawagar ‘yan sanda ta yi isa wurin, inda aka ceto fasinjoji hudu da ransu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 5 Ne Suka Rasu, Yayin Da Gidaje 3,813 Suka Ruguje A Katsina
Ya kuma kara da cewa, sauran fasinjoji biyar sun nutse a cikin kogin sannan ‘yan sanda sun gano gawarwakinsu tare da mika su ga ‘yan uwansu domin yi musu jana’iza.
A WANI LABARIN KUMA: Sojoji Na Gudanar Da Bincike, Haɓakawa Don Magance Kalubalen Tsaro A Kasa
Rundunar Sojin Najeriya ta jaddada kudirinta na gudanar da bincike da ci gaba don magance kalubalen tsaro da ke addabar al’ummar kasar yadda ya kamata.
Mejo janaral Abdulsalam Ibrahim, Shugaban Horaswa (Sojoji) ya sake nanata hakan a wajen bude taron bincike da ci gaba na shekarar 2022 da daidaita tsarin karatu ga Makarantun Sojojin Najeriya a ranar Litinin din nan a Abuja.