Hukumar dake kula da tituna ta sanar da kididdigan aukuwar hadura dubu biyar da dari uku da ashirin, a inda kimanin mutane dubu biyu da dari hudu da saba’in da daya suka rasa rayukansu sanadiyyar hadarurrukan Motoci a cikin watanni shida. Kamar yadda Jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta
Jami’i mai wayar da hankullan mutane game da hadura Marshal (ACM), Mr Bisi Kazeem, ya bayyana haka a wani zantawa da yayibda manema labarai a ranar Litini a Abuja.
Mista Kazeem, yace a gaba dayan kididdigan ya auku ne a cikin watanni shida kacal tun daga January zuwa June na wannan shekarar, duk da iya bakin kokarin da hukumar keyi don ganin an takaita yawan aukuwar haduran.
KARANTA:- Duk wanda zai aureni to ya tabbata sai mamansa ta mutu tukunna, cewar Wata Matashiya
A gaba daya haduran 5,320 da suka auku a kasar ya hada da Motoci 8,808, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane 2,471.
Ya Kara da cewa mutane15,882 suka sami raunuka, inda mutane 15,398 suka kubuta daga Jin manyan raunuka a yayida haduran suka auku.
Wannan ya bada jumillan mutane 33,751 suka gamu da hadura a cikin watanni shida tun daga January zuwa June na wannan shekarar.
Mista Kazeem, yace a yayin kididdige haduran, yace cikin watan January kadai an sami hadura 963 a gaba dayan kasar.
A dai jahohin Kaduna, Kano, Katsina and Jigawa, inda haduran yafi aukuwa an sami 148.
Mista Kazeem, yace hukumar ta damke mutane 251,005 a tsakanin watanni shida, inda suka karya dokoki 281,786 na kan hanya a gaba daya kasar.
Yace naurar da hukumar ta kaddamar ta kama dubbanin masu laifuka a kasar nan.
Wadanda dai aka kama da laifin an damka su zuwa kotu inda suka fuskanci hukunci daidai da abunda suka aikata.
Comments 1