Daga: Abbas Yakubu Yaura
Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kusa da gadar Isara, Ogere, kusa da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a daren ranar Asabar.
Wasu mutane bakwai sun samu raunuka mabambanta a gobarar da ta yi sanadiyar hatsarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/zamfara-apc-ta-zargi-pdp-da-yin-zagon-kasa-ga-matakan-tsaro-da-gwamna-matawalle-yake-dauka/
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Mista Ahmed Umar, ya tabbatar da alkaluman mutanen da hatsarin ya rutsa da su ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abeokuta.
Umar ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 10.35 na dare.
A cewar sa “Motoci biyu Mazda da wata mota hatsarin ya rutsa da su sakamakon wuce gona da iri a yayin tuki.
Ya kara da cewa motocin da abin ya shafa sun kone tare da wadanda suke ciki inda suka mutu ba tare da tantancewa ba.
An kai shida daga cikin mutane bakwai da suka jikkata zuwa wani asibiti da ke Ogere domin yi musu magani, yayin da mutum na bakwai kuma an kai shi asibitin koyarwa na jami’ar Babcock da ke Ilisan, shi ma a Ogun domin yi masa magani.
Umaru ya ce wadanda suka jikkatan manya ne maza biyar, babbar mace daya da yaro namiji.
“An shawarci masu ababen hawa da su yi tuƙi a hankali, su yi biyayya ga dokokin hanya da kuma yin aiki tare da masu kula da ababen hawa,” in ji shi. (NAN)