Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 7 a Osun
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa reshen Jahar Osun tace mutane bakwai sun mutu a haɗurra daban-daban a watan Mayu.
Kwamandan Shiyya na Hukumar Paul Okpe ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun sa ya fitar Agnes Ogungbemi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗuminsa: Bayan Janye wa Tinubu, Akpabio ya samu Tikitin Takarar Sanata a APC
Okpe yace Haɗurra guda 26 ya hallaka rayuwar mutane 7, tare da barin mutane 26 da raunuka.
A cewar sa, Rundunar ta kuma kama mutane 375 da suka karya Dokokin hanya a faɗin Jahar, a yayinda wasu mutane 125 aka ilmantar dasu akan dokokin hanya.
Okpe yace Hukumar ta bada lasisin tuƙi ga masu motoci, inda ake da wasu da basu karɓa ba.
“Adadin yawan lasisin mota da aka bada da wanda ba’a karba ba yakai 4,074,” Inji shi
Comments 1