Wata mata da ‘ya’yanta guda biyu a ranar Lahadin da ta gabata sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a tsohuwar tashar MRS da ke unguwar Itako a yankin Ijebu-Ife daura da babbar hanyar Sagamu zuwa Benin a jihar Ogun.
Hadarin ya rutsa da wata motar Dangote mai lamba: WW 630 XA da Ford jeep mai lamba AKD 311 HH.
Rahotanni sun nuna cewa mamaciyar na tafiya Gabas ne domin hutu a lokacin da hatsarin ya afku.
A cewar wani ganau, Motar kirar kirar Ford jeep tana kan hanyarta ne daga Legas zuwa yankin gabashin kasar nan, domin hutu, sai ta kutsa kai cikin wata motar Dangote dake tsaye daga a gefen hanya.
Jami’in hulda da jama’a (PRO) na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Ogun (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta, babban birnin jihar.
Akinbiyi ya alakanta musabbabin faruwar hatsarin da gudun wuce gona da iri da kuma rashin kula daga bangaren direban motar kirar jeep din.
“An ruwaito cewa direban motar yana tuka marigayiya da ‘ya’yanta mata guda biyu zuwa yankin Gabashin kasar nan ne, a lokacin hutu, sai hatsarin ya faru.
“Mijin matar yana kasar waje kuma direban yana aiki a matsayin direban dangi ne,” in ji Akinbiyi.
Ya kara da cewa an kai motocin zuwa ofishin ‘yan sanda na Ijebu-Ife domin ci gaba da bincike yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Asibitin Goshen.
Mai magana da yawun TRACE, yayin da yake jajantawa iyalan mamatan, ya bukaci direbobi da su guji gudun wuce gona da iri da tukin ganganci, musamman a wannan lokaci na hunturu.