By Ishaq Dabai
Hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC reshen jihar Adamawa, tace akalla mutane 62 ne suka mutu yayin da 624 suka jikkata a hatsarin mota tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na shekarar 2021 a jihar.
Mista Utte Boyi, Kwamandan shiyyar, shine wanda ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Juma’a a birnin Yola.sannan yace a lokacin da ake nazari, mutane 1,025 da ababen hawa 369 sun shiga cikin hadurran hanyoyi 202 da akasarinsu ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da direbobi keyi.
Sannan ya bukaci masu amfani da hanyoyin da su kasance masu bin ka’idodin zirga -zirgar ababen hawa a koda yaushe da kuma gujewa tafiye -tafiyen cikin dare don rage yawan hadurra, musamman a cikin watanni masu zafi.a yanzu haka “Mun shiga watanni masu dumbin yawa kuma lokaci ne na gaggawa saboda mutane da yawa za su yi balaguro sa kamakon karatowar watan disamba.
“Don haka bai kamata masu motoci su yi gaggawar daukar fasinjoji dan samun kudi mai yawa ba.”A zahiri, yakamata ku sanya na’urar iyakance gudu a cikin motocin ku don taimaka muku sarrafa saurin abin hawan ku,” in ji shi.
Boyi ya kuma bukaci direbobi da su guji wuce gona da iri don gujewa kara matsa lamba kan tayoyin abin hawan su, wanda hakan na iya haifar da fashewar taya da afkuwar hadari.