Hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Ogun ta bayyana cewa, wani hatsarin mota da ya afku a kasuwar Mile 12, Ogere, da ke kan titin Legas zuwa Ibadan, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu takwas a daren jiya Asabar.
Kwamandan sashin, Mista Ahmed Umar ne ya tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a Abeokuta a safiyar yau Lahadi.
Umar ya ce wata Mota mai lamba BR 446 XE tana gudu ne a lokacin da ta bugi tsakiyar hanya, inda ta fadi a da misalin karfe 7:18 na dare.
A cewarsa, motar na dauke da buhunan sukari yayin da wasu daga cikin wadanda abin ya shafa ke zaune a kan buhunan kafin faruwar lamarin.
Shugaban FRSC ya bayyana cewa mutane 15 ne hatsarin ya rutsa da su, wadanda suka hada da maza 14 da mace daya.
Ya bayyana cewa mutane takwas da suka jikkata dukkansu maza ne, inda ya ce mutane biyu ne suka mutu a hatsarin.
Umar ya ce an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Asibitin FOS da ke Ipara, yayin da wadanda suka jikkata aka kai su Asibitin Victory Ogere domin yi musu magani.
Kwamandan sashin ya gargadi masu ababen hawa kan gudun wuce kima da kuma tuki mai hatsari