Wani hatsarin mota da ya auku a kusa da garin Jakusko da ke Jihar Yobe ranar Lahadi ya yi sanadiyar rasuwar mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama.
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Toyota Hiace mai daukar mutum 18, wacce ta yi taho-mu-gama da wata karamar mota samfurin Honda da misalin karfe 10:00 na safe.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar hatsarin ya faru ne yayin da motar Bus din da ta so daga garin Potiskum zuwa Gashuwa ta ci karo da Hondar, wacce ita kuma ta fito daga garin na Gashuwa, inda nan take motocin suka kama da wuta, Kuma suka Kone kurmus.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin Shugaban Karamar Hukumar Jakusko, Abdullahi Gwayo ya bayyana cewa, tuni Karamar Hukumarsa ta dauki nauyin kai wadanda suka samu raunukan Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Azare a Jihar Bauchi da kuma Asibitin Tarayya da ke Nguru (FMC) a Jihar ta Yobe, domin samun cikakkiyar kulawar likitoci.