By Abbas Yakubu Yaura
Mista Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a Bauchi, yace akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota daya afku a Bauchi ranar Lahadi.
Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi a Bauchi, ya bayyana cewa wasu mutane shida sun samu raunuka daban-daban.
Sannan yace hatsarin ya rutsa da wata motar bas mai lamba GSH 42 AA, inda hatsarin ya afku kilomita daya bayan Kasuwar Durum dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano da karfe 9:53 na safe.
Kwamandan sashin, wanda ya ce sai da jami’an hukumar suka dauki kimanin mintuna 12 kafin su isa wurin domin share wurin, ya alakanta hatsarin da keta haddin hanya da kuma fashewar taya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hatsarin ya rutsa da mutane takwas inda suka hada da maza biyar, mata biyu da yaro namiji daya.
“Mutane biyu sun mutu nan take, wasu shida kuma sun samu raunuka. Sun hada da maza uku, mata biyu da yaro namiji daya,” inji shi.
Abdullahi ya ce an bayyana sunan direban motar mai suna Ibrahim, ya kara da cewa an mika wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUH) da ke Bauchi domin yi musu magani.
Kazalika ya bayyana cewa an kuma ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na wannan asibitin domin tantance su.
Kwamandan sashin ya shawarci masu ababen hawa da su kasance masu bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kodayaushe yayin da suke bin hanyoyin.