By Ishaq Dabai
Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da cewa mutane 11 ne suka rasa rayukansu a wani Hadarin Mota daya afku a ranar Lahadi a jihar Kwara.
Kwamandan Yankin Kwara na Rundunar, Jonathan Owoade, wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Ilorin, yace hadarin ya afku ne a hanyar Jebba-Bode Saadu.inda Owoade ya kara da cewa hadarin ya shafi wata mota kirar Toyota Corolla mai lamba AAA 250 CB da wata motar Toyota Hiace mai lamba LAP 179 XA.
Sannan yace yayin da mutane 26 ke cikin hatsarin, mutane 15 sun jikkata sannan mutane 11 sun rasa rayukansu.“A yammacin ranar lahadi mun samu kiran gaggawa na hatsarin da ya faru da misalin karfe 4 na yamma a kauyen Onipako, a kan hanyar Bode-Saadu-Jebba.
Kazalika Kwamandan sashen yace an kai wadanda suka jikkata asibitin Jebba da asibitin Emmanuel Jebba, yayin da aka ajiye gawarwakin a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH).Owoade yace an share shingen daya haddasa hadarin kuma akwai zirga -zirgar ababen hawa kyauta.