Sabuwar Jami’ar Gona ta Gwamnatin tarayya dake Zuru a jihar Kebbi ta gargadi al’umma cewa da su yi hattara da ‘yan damfara da suke amfani da shafin boge a shafukan sada zumunta da sunan Jami’ar.
Abdulaziz Yusuf-Bazata, Magatakardar Jami’ar shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi a ranar Talata.
Yusuf ya kara da cewa; hankalin Jami’ar ya karkata ne ya zuwa wata talla da ake yadawa cewa Jami’ar na daukar ma’aikata, “inda ake yada batun a shafukan sada zumunta, ana neman masu neman aiki a Jami’ar su tura bukatar hakan zuwa wani adireshin Imel na oyewaleao@gmail.com.” Jami’ar ta ce; wannan sam ba gaskiya bane, su ba su neman ma’aikata a yanzu. “Babu wani abu makamancin hakan da yake gudana a Jami’ar.” Ya tabbatar.
Ya karkare da cewa; “Jami’ar na nesanta kanta da wannan talla na shafukan sada zumunta, domin ba daga Jami’ar tallar yake ba.” ya karkare.
A karshe sun shawarci al’umma da su yi watsi da wannan tallar tare da hankali da ‘yan damfara.