Gwamna David Umahi ya bayyana aikace-aikacen Ƙungiyar Tsagerun Kafa Ƙasar Biafra IPOB a matsayin shirme ne.
Ƙungiyar wadda aka ɗorawa alhakin aikace-aikacen ta’addanci a yankin Kudu maso Gabas, suna cigaba da neman a tsage masu Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Bindiga sun saki Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Jahar Nasarawa
Ƙungiyar tana ayyana Dokar zaman gida na sati-sati a matsayin wani sadaukar wa ga Shugaban ta Nnamdi Kanu, wanda a halin yanzu yana a kurkukun DSS.
A lokacin Dokar Zaman, dukkanin mutanen da aka gani akan hanyoyi, akan kai masu hari.
Dayake tsokaci akan wannan ta’addanci da wasu Editoci, Umahi yace “ina so inyi amfani da wannan inyi kira Inyamurai da su zama masu hankali, wannan zaman gidan shirme ne, kuma Hauka ne. Wannan neman Kafa Ƙasar Biafra hauka ne a gareni, domin koda za’a kafa Ƙasar Biafra, to Ebonyi Bata daga ciki.
“Mu ƴan Biafra bane ba, muna Son Zaman Lafiya kuma dai-dai muke da kowane Ɗan Najeriya. Ina so in Cigaba da kira cewa babu alfanu a zaman gidan nan, babu wani amfani a kashe kanmu, kuma ina ganin faɗa damu da wasu ƴan yanki abune da wuce. Muna zama lafiya da ƴan uwa a wasu ɓangarori kuma yana cigaba. Amma zaman gida, ban goyi baya ba, kuma ina so mu fito muyi wani abu akan Al’ummar mu.