Al’ummar Hausawa a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i da ya ƙirƙirar musu da sabuwar masarauta.
Mutanen yankin ƙarƙashin wata ƙungiyar kare haƙƙin al’ummar yankin mai suna Cibiyar Na-Tanko ta ce Hausawan da ke ƙananan hukumomin Chikun, Kajuru, Sanga, Kauru, Kagarko, Zangon Kataf da kuma Lere na buƙatar masarauta domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiyar yankunan.
Jagoran ƙungiyar, Alhaji Aminu Idris da sakatarenta Yusuf Muhammad Yunus a wata sanarwa sun ce, “Al’ummarmu na ci gaba da miƙa ƙoƙon barar ƙirƙirar sabuwar masarauta ga Hausawan Ƙaramar Hukumar Chikun kamar takwarorinsu na wasu yankunan.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-mutane-20-a-zangon-kataf-dake-jihar-kaduna/
“Muna so mu bayyana ƙarara cewa gundumarmu ba ta taba kasancewa ƙarƙashin yankin Kudancin Kaduna ba, kuma duk wani yunƙuri na duk mai son cimma wata manufar siyasa ta hanyar shigar da ƙananan hukumomin Chikun da Kajuru yankin ba ya kan ƙa’ida saboda a Kaduna ta tsakiyar suke,” inji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma yaba wa ƙoƙarin gwamnan jihar da kantomar ƙaramar hukumar ta Chikun, Hajiya Hadiza Ladi Yahuza kan abun da suka kira ƙoƙarin da su ke yi na ceto yankunan da ake wa danniya a jihar da kuma tabbatar da zaman lafiya.