A ranar Alhamis ne hukumar ‘yan sanda a jihar Legas ta bayyana samun gawar wasu mawaƙa guda biyu, da misalim ƙarfe bakwai na safe bayan shafe dare suna aikin waƙa a anguwar Alagbado dake jihar ta Legas.
Mawaƙan masu suna Ajibawo Lawal da Sunday Akhigbe, ana zargin hayaƙin Inji da kuma kayan maye da suka sha ne yayi sanadin rasuwarsu.
Wani magidanci mai suna Mahfuz Majeed wanda mazaunin yankin ne, ya shaidawa manema labarai, “sun bar inji yana ta aiki tun cikin dare har wayeear gari, da muka ga alamun matsala sai muka balle kofar ɗakin kiɗan nasu ko da muka shiga sai muka tarar mutane biyu sun rasu biyu kuma suna cikin wani mawuyacin hali nan take muka ɗauke su zuwa asibiti.”
Sai dai hukumar ta ‘yan sanda tace za lta binciki manajan mawaƙan da zarar ya farfaɗo domin samun cikakken rahoton abinda ya faru.